Kungiyar lauyoyi ta kai karar majalisar dokokin Najeriya

Kakakin majalikar wakilan Najeriya,Dimeji bankole
Image caption Kungiyar lauyoyi ta kai karar 'yan majalisar Najeriya

A Najeriya, kungiyar lauyoyi ta gurfanar da majalisar dokokin kasar gaban wata babbar kotu dake Abuja bisa irin kudaden da ake biyan 'yan majalisar.

Kungiyar lauyoyin dai na bukatar dakatar da biyan albashi da kuma alawus ga 'yan majalisar, wanda ta ce ya sabawa abinda hukumar tattara kudin shiga tare da rabasu wato Revenue Mobilisation Allocation and Fiscal Commission a turance, ta kayyade.

A karar da kungiyar lauyoyin ta shigar, har da akawun majalisar dokokin da Ministan Kudi na kasa da babban Akanta da kuma ministan shari'a.

Sai dai su kuma 'yan majalisar sun musunta tuhumar da ake musu, inda suka ce ba sune ke da alhakin baiwa kansu albashi ba.