Dan sanda yayi garkuwa a birnin Manila

motar da aka yi garkuwa da ita a Phiippine
Image caption motar da aka yi garkuwa da ita a Phiippine

An kawo karshen garkuwar da aka kwashe tsawon sa'o'i tara ana yi da wata motar safa mai dauke da wasu 'yan yawon bude ido a Manila, babban birnin Philippine, inda wasu daga cikin fasinjojin suka yi rarrafe suka fito daga motar.

Babu cikakken bayani kan abin da ya faru da saura fasinjojin, galibinsu 'yan yawon bude ido daga Hong kong, amma akwai wasu kafafen yada labarai dake cewa bakwai daga cikinsu sun rasa ransu, bayan da 'yan sanda suka kutsa kai cikin motar, aka kuma yiayar harbe harbe.

Wani tsohon dan sanda ne, dauke da bindiga, ya yi garkuwa da mutanen, yana mai cewar ransa ne a bace, saboda an kore shi daga aiki. 'Yan sanda sun ce an kashe dan bindigar.