Najeriya na janye lalatattun jirage daga gabar teku

Taswirar Najeriya
Image caption Hukumomi na janye lalatattun jirage daga gabar teku

Hukumar kula da tsaron tekun Najeriya,wato NIMASA a turance,da hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa NPA, sun fara janye manyan jiragen ruwa da su ka lalace, bayan tsawon shekaru da su ka dauka suna tsaye a gabar tekun kasar.

A na zargin cewa jiragen da suka lalace din dai na haddasa gurbatar muhalli da kuma cunkoso a gabar tekun.

Kazalika,hukumomin sun ce tsayuwar manyan jiragen, wata barazana ce ga harkokin kasuwanci a gabar ruwan kasar.

Najeriya na fuskantar rashin tsaro a iyakokin ruwanta.