An kawar da tasirin da Taliban ke yi a Afghanistan,inji Petraeus

Dakarun Amurka dake Afghanistan
Image caption Janar Petreus ya ce an kawar da tasirin kungiyar Taliban daga wasu sassan Afghanistan

Kwamandan dake jagorancin rundunar NATO a Afghanistan, Janar David Petreus,ya ce an kawar da tasirin da kungiyar Taliban ke da shi a kudancin kasar, da kuma babban birnin Kabul.

A daya daga cikin hirarrakinsa na farko tun bayan da ya fara jagorancin rundunar, Mista Petreus ya shaidawa BBC cewa, zai gayawa shugaba Obama cewa shirin Amurka na janye dakarunta daga Afghanistan a badi ya yi wuri.

Janar Peterus nada kwarin giwa cewa zai kawo sauyi a kasar ta Afghanistan, kasancewarsa mutumin da ake gani yayi sanadiyar kaiwa ga nasara yakin kasar Iraqi.

Wani abu da yake alfahari da shi shi ne,Washington bata yi masa katsalandan a al'amuransa.

'Zai baiwa shugaba Obama shawara'

Ya ce zai shaidawa shugaba Obama cewa shirin kasar na fara janye dakarunta daga kasar, a watan Yulin shekara mai zuwa na cike da hadari.

Amma da aka tambaye shi, shin baya ganin za a yi kokarsa daga aikin,kamar yadda aka yiwa wanda ya gada, sai ya ce ai duk wanda ya fara irin wannan aiki to a shirye yake da ya barshi.

Ya yi fatali da zargin da ake cewa Amurka ta kawar da kai daga Afghanistan, inda sabanin hakan ta mayar da hankali wajen mamaye Iraqi.

Ya ce ya taba shaidawa Sakataren tsaron Amurkan da ya gabata, wato Donal Rumsfel cewa yakin Afghanistan ba na kare bane.