Janar din Amurka ya zafafa muhawarar janye dakaru daga Afghanistan

Shugaba Barack Obama
Image caption Shugaba Barack Obama

Wani babban janar na sojin Amurka ya bayyana cewa wa'adin da shugaba Obama ya bayar na fara janyewar dakarun Amurka daga Afghanistan a watan Yuli na shekarar 2011, na karfafawa mayakan Taleban gwiwa.

To sai dai shugaban dakarun sojin Amurka Janar James Conway, ya ce za a iya sauya wannan wa'adi , idan sojojin Amurka suka ci gaba da kai hari bayan karewar wa'adin.

Ya ce, "makiyanmu su ma sun fara gajiya, suna gurzuwa fiye da mu sosai. Su na kuma tambayar kansu, wai anya kuwa sun cancanci hakan, su na yi wa kansu wannan tambaya a halin yanzu".

Ya kara da cewa sojojin kasa na Amruka a kudancin kasar zasu cigaba da kasancewa zuwa wasu 'yan shekaru.