Ambaliyar ruwa: Mutane sun fara kokawa a Ghana

Taswirar Ghana
Image caption Taswirar Ghana

A kasar Ghana a yayin da ake ci gaba da kokarin kauce ma irin bannan da ambaliyar ruwan da ta biyo bayan bude madatsan ruwan Bagre Dam da kasar Burkina Faso tayi a ranan Jum'a da ta wuce wasu mazauna wasu wuraren da ambaliyar ruwan ta shafa sun fara kokawa kan yadda take rabasu da gonaki da kuma gidajensu.

A fira da sukayi da wani gidan radiyo mai zaman kansa dake birnin Accra wato Joy FM mutanen sunce idan dai ba dauki aka kawo musu ba to tasu ta kare kenan. Lamarin dai yafi kamari ne a gunduman Talensi Nabdam dake arewa maso gabashin kasar.

Rahotannan dake fitowa daga wajen dai sunce wasu cikin mazauna wajen sun nemi mafaka wajen 'yanuwansu da gine ginen makarantu da kuma tasoshin mota bayan da ambaliyar ruwan ta malale musu gidaje da gonaki.

Mutane sun shiga matsala

"Iyali na basu da abinda zasu ci. Yaya kenan zamu yi. Ruwan ya malale min gona; gida na kuma gashinan ya lalace. Muna kira ga gomnati don Allah ta kawo muna dauki." Inji daya daga cikin mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa. Shima wani da ambaliyar ruwan ta shafa ya kara da cewa;

"Zamu iya tashi zuwa wasu wuraren daban to amma ba zamu iya dauke gonakinmu ba. Ina cikin manyan manoman dake noma a nan wajen. Dubi gona ta; yaya mutun zeyi noma cikin ruwa, hatta wannan gidan dake nan ma ruwan ya malaleshi. Yaya zamu yi da wannan lamari."

Manjor Nicholas Mensah mai ritaya kakakin hukuman bada agajin gaggawan kasar wato NADMO, ya bayana irin kokarin da gwamnatin kasar keyi domin taimakawa mutanen;

"Mutanen mu na nan suna kai suna kawowa ko ina don gano wadanda lamarin ya shafa. A jiya sun kai dauki a wasu wuraren. A yau ne za su isa wajen mutanen. Da zarar sun isa wajen za'a shawo kan wannan matsala."

Kokarin gwamnati

Manjo Nicholas Mensah yace Idan bala'i irin haka ya auku ba kawai zuwa ake a jibge kayan agajin ba, sai an gudanar da bincike don gano wadanda suke bukata da kuma irin kayayyakin da za'a kai musu.

"Kamata yayi kuma mazauna wuraren suyi aiki da gargadin da ake musu don ganin ba'a samu banna da yawa da kuma asarar rayuka ba." In ji Manjo Nicholas Mensah

Ya ce babu alamar cewa ambaliyar ruwan zata yi banna sosai a bana. Sai dai masu lura da al'amura na ganin cewa abubuwan da zasu auku a 'yan kwanaki masu zuwa, su ne kawai zasu iya yanke wannan hukunci.