Gwamnatin Pakistan na tattaunawa da asusun bada lamuni

Jama'ar kasar na cikin wani hali saboda ambaliyar ruwa
Image caption Jama'ar kasar na cikin wani hali saboda ambaliyar ruwa

Jami'an gwamnatin Pakistan sun fara tattaunawa da asusun bada lamuni dake don karbar bashi.

Hakan na zuwa ne a yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar mummunar ambaliyar ruwa a tarihinta.

Asusun bada lamini na IMF ya baiwa kasar ta Pakistan kwarin gwiwa a karshen mako cewa,inda ya ce yana tare da ita a cikin wannan matsanancin hali da take ciki.

Sai dai jami'an gwamnatin Pakistan na saran samun kudi ne daga asusun kafin su yarda da wannan kalami na asusun.

Kafin a yi ambaliyar ruwan,asusun bada lamunin ya amince ya baiwa kasar bashin kimanin dala biliyan goma sha daya.

Sai dai yanayin tattalin arzikin kasar ya sa an dakatar da batun.

Don haka yanzu dai abin yi shi ne,ko dai Pakistan ta sake sabon kudiri na neman bashin,ko kuwa ta nemi agajin kudi na gaggawa daga wajen asusun bada lamunin.

Yayin da hakan ke faruwa,a can lardin Sindh,ruwan kogin Indus ya kai cika makil,inda ake ganin zai tumfaya a yau talata.