Akwai damuwa ta samun karin yaduwar cutuutuka

A daidai lokacinda hukumomin kasar Pakistan ke ci gaba da kokarin shawo kan matsalolinda balain ambaliyar ruwa ya haddasa, Pirayim Ministan kasar Yousuf Raza Gilani, ya ce yana da matukar damuwa bisa yiwuwar yaduwar annoba.

A lokacinda yake jawabi a wani taron kwararru kan harkokin lafiya, Mr Gilani ya bayyana wasu daga cikin kalubalolin lafiya da kasar ke fuskanta.

A cewarsa, likitoci da dama da kuma fiye da rabin maaikatan lafiya mata na kasar na daga cikin miliyoyin mutanenda suka rasa muhallinsu.

Ana sa ran kuma mata kimanin million guda ne za su haihu a yankunanda ambaliyar ruwan ta shafa a tsakanin nan da watanni shidda masu zuwa.