Al Shabab ta kashe sama da mutane 30 a Otal

Mayakan kungiyar Al shabab
Image caption Mayakan kungiyar Al shabab

Mayakan Islama a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, sun ce su ne ke da alhakin kai hari akan wani otel wanda yayi sanadiyyar rasuwar mutane fiye da 30, ciki har da yan majalisar kasar.

Kakakin kungiyar al-Shabaab din, ya ce dakarunsu na musamman ne suka kai hari akan masu taimakawa Kafirai kamar yadda ya fadi.

Sai dai kakakin dakarun samar da zaman lafiya a Somalia Major Bahoku Barigye, ya ce wannan hari ya nuna gazawar al-Shabaab ne.

Ya ce, "bai kamata wannan ya baiwa kowa mamaki ba. Abu mai muhimmanci a wannan alamari shine cikin watanni biyunda suka gabata sun yi ta kokarin kai hari akan sansanoninmu da wuraren gwamnati, amma hakarsu bata cimma ruwa ba".

Rikici a birnin Mogadishu ba abin abu bane sabo amma fadan baya bayannan daban yake bawa kawai dangane da girman rikicin ba amma dangane da irin mahimmancinsa.

An fara ne bayanda wani mai magana da yawun Al Shabab Sheikh Ada Mohammad rageh ya bayyana abinda ya kira sabon yaki da masu mamaya. Ana dai tunanin akwai dakarun Afrika da tuni yawansu ya kai mutum dubu shidan a kasar.

Hari a arewacin Mogadishu

Fadan dai yafi karfi ne a wasu yankuna a arewacin birnin Mogadishu inda har yanzu ke karkashin ikon gwamanti da kuma wasu kewayenta na cikin gida.

Zaiyi wahala a iya cewa ga ainihin yawan mutanen da fadan ya lahanta amma maikatan kuiwon lafiya a garin sunce akalla mutane arbain sun mutu mafiyawancinsu fararen hulane hakazalika an juikkata wasu da dama.

A wani hari da aka kai a wani otal 'yanbindiga sun kashe akalla mutuane talatin da daya wadanda suka hadada mambobin majalisa shida da kuma dakarun gwamanti su biyar.

Ministan yada labaran somaila Abdurahman Omar ya shaidawa BBC cewar ; "Wasu 'yan kuna bakin wake biyu daga Al Shabab sunzo yau zuwa otal din Mona a mogadishu kuma sunyi ta harbin kan mai uwa dawabi."

Fadan dai ya biyo bayan karuwar rade raden da ake tayi na rashin bada hadin kai ga gwamantin rikon kwaryar kasar. idan har dakarun tarayyar Afirka za su ci gaba da zama sojoji masu sharhi sunce da wuya 'yan tawayen su iya kwace iko amma idan har goyan bayan da gwamanti take samu ya kau kuma gwamnatin ta rushe to lallai suma dakarun tarayyar afrikan zasu tatara yanasu yanasu.