Babban Bankin Nigeria ya ce zai saki Naira biliyan 300

Malam Sanusi Lamido Sanusi
Image caption Malam Sanusi Lamido Sanusi

Babban bankin Nigeria ya bada sanarwar cewa a shirye ya ke ya saki Naira biliyan 300 na wani asusun musamman da aka ware domin bayar da bashi da nufin bunkasa harkokin wutar lantarki da sufuri ta jiragen sama.

Babban bankin na Nigeria ya bullo da sharudda wajen bayar da wadannan kudade.

Ana sa ran kudaden za su bi ta hannun Babban bankin masana'antu na Nigeria wato Bank of Industry.

Wadannan kudaden dai wani bangare na kudaden tallafin Naira Biliyan dari biyar da bankin ya ce zai bayar tun a watan Aprilun da ya gabata, domin zaburar da tattalin arzikin Nigeria.