Ban Ki-Moon ya fusata kan fyade a Congo

Babban Sakataren majalisar dinkin duniya,Mista Ban Ki Moon
Image caption Mista Ban Ki Moon ya nuna bacin rai kan fyade a kasar Congo

Babban sakataren majalisar dinkin duniya, Mista Ban Ki-Moon ya ce fyaden da kungiyar 'yan tawaye a kasar Congo su ka yiwa wasu mata guda 154 ya bata masa rai.

Ya tura wani babban jam'in majalisar zuwa kasar ta Congo,inda zai tattauna da gwamnati kan batun fyaden wanda aka yi makonnin da dama da suka gabata.

'Yan tawayen sun yi fyaden ne a kusa da wani karamin sansanin ma'aikatan majalisar Dinkin Duniya dake kasar,abinda alamar rauni ce ga aikin da majalisar keyi a kasar.

Kai harin wani abin haushi koda kuwa a wannan kasa da fyade ya zama wani makami da 'yan tawaye ke amfani da shi don cin zarafin mata.