Ghana zata shiga sahun kasashe masu arzikin man fetur

Kasar Ghana tace a cikin watan Disambanwannan shekarar ne zata shiga kungiyar kasashen duniya masu arzikin man fetur bayan ta fara hako danyen man fetur da ta gano cikin kasar don sayarwa a kasuwannin duniya.

Mataimakin shugban kasar wato John Mahama wanda ya fadi hakan a jiya a wajen wani taron bita na yini guda da aka gudanar a birnin Accra.

An yi taro ne kan gajiyar da kasar zata ci daga arzikin man fetur.

Mataimakin shugaban yace kiyasin baya bayan nan da aka fitar ya nuna cewa adadin danyen man fetur da kasar take dashi a karkashin kasa ya kai sama da ganga miliyan dubu guda da rabi.