Hare-Haren bama bamai a Iraqi sun hallaka mutane akalla 50

Hari a Iraqi
Image caption Hari a Iraqi

Mutane fiye da 40 sun hallaka sannan wasu fiye da 200 sun samu raunika, a wasu jerin hare hare da aka kai da bamai bamai a wurare daban daban a kasar Iraqi.

An kai hare hare akalla 12, wadanda suka hada da bama baman da aka dana a motoci da kuma a gefen tituna.

Akasari an yi hakon dakarun tsaro ne a wadannan hare haren.

Tashin bamb a birnin Kut dake kudu maso gabacin kasar ne ya fi haddasa mummunar barna, inda mutane akalla 50 suka mutu.

A Bagadaza babban birnin kasar kuwa, mutanen 15 ne suka hallaka a wani hari da ak akai a arewacin birnin.

Haka nan kuma an kai hare hare a Kirkuk da Basra da Ramadi