Mutane hamsin sun halaka a Iraq sakamakon hare-hare

A kalla mutane 50 ne suka halaka, kuma kimanin 250 suka jikkata sakamakon wasu jerin hare-hare a wurare daban daban na kasar Iraqi.

Bama-baman da suka fashe dai sun kai 12, a motoci da gefen tituna, inda kusan dukkaninsu na harar 'yan sanda ne.

Ministan kula da harkokin wajen Iraqi Hoshyar Zebari, ya bayyana cewa shirin janyewar dakarun Amurka daga fagen daga shi ne ke karfafawa masu tada kayar baya gwiwa.