Kungiyar tarayyar turai ta tallafawa Nijar

Wasu mutane da ambaliyar ruwa ta shafa a Nijar
Image caption Tarayyar turai ta tallafawa wadanda yunwa da ambaliyar ruwa ta shafa a Nijar

A jamhuriyar Nijar, kungiyar tarayyar Turai ta baiwa kasar gudunmawar kimanin euro miliyan goma sha biyar .

Kungiyar ta ce ta bada tallafin ne domin kasar ta tunkari al'amarin yunwa da wasu 'yayanta ke ciki.

'Yan nijar din dai sama da miliyan bakwai ne ke fuskantar matsalar karancin abinci a bana.

Kazalika wasu sun fada cikin mawuyacin hali sakamakon ambaliyar ruwa da ta ruguje gidajensu.