Ambaliyar ruwa a Pakistan na kara yin barazana

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Pakistan

Ruwan da ke toroko wanda ke malala daga arewaci zuwa kudancin kasar Pakistan na yin barazana ga wasu sabbin wurare a lardin Sindh na kasar.

Baya ga irin mummunar matsalar da wannan abu ya haifar ga jama'a masu dymbin yawa, a yanzu akwai fargabar ambaliyar ruwan zata iya kara haddasa asarar amfanin gona da dabbobi wadanda marassa galihu suka dogara da su.

Shugaban hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, Daniele Donati ya bayyana cewa ruwan ya lalata abinci mai yawa da ya hada da shinkafa da masara da kayayyakin lambu.

Haka kuma kayan irin da aka tanada domin shukawa suma duk sun salwanta.