An kashe yara biyar a Afghanistan

Taswirar kasar Afghanistan

Hukumomi a gabashin kasar Afghanistan, sun ce an kashe wasu yara biyar a wani hari da aka kai ta sama a lardin Kunar.

Wani jami'ain 'yan sanda a yankin ya ce, yaran suna tattara itatuwa ne a kan wani tsauni lokacin da aka kai musu harin da ya yi sanadiyar ajalinsu.

Wani rahoton kuma na nuni da cewa, masu tada kayar baya sun harbe wani yaron.

Sojojin kasashen duniya karkashin jagorancin NATO sun ce, tabbas sun kai hari a yankin, sai dai basu da tabbacin harin ya shafi fararen hula.

Sai dai wani mai magana da yawun NATON, ya ce za su bincika zargin.