Goodluck ya bayyana sabon shirin samar da lantarki

Layin wutar lantarki
Image caption Layin wutar lantarki

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya bayyana wani shirin da zai ci biliyoyin daloli da nufin gyara bangaren wutar lantarki na kasar mai fama da matsaloli.

A karkashin shirin Shugaba Goodluck Jonathan ya ce kasar za ta sayar da Kamafanin samar da wutar lantarki na kasar kuma ma'aikatansa za su samu hasafin sallama mai tsoka.

A cikin wani jawabi da yayi ga yan jarida da kuma masu fada ajin siyasa na kasar a Lagas, Shugaba Jonathan ya ce kasar za ta dogara a kan kamfanoni masu zaman kansu domin gina sababbin tashoshin samar da wutar lantarki.

Shugaba Jonathan ya ce kasar na bukatar wani juyin juya hali a harkar samar da makamashi a kasar, yana mai alkawarin cewar 'yan Nigeria zasu samu karin hasken wutar lantarki a watan Disamba na shekara ta 2012.

'Yan Najeriya dai na fama da matsalar dauke wutar lantarki a kowacce rana.

Karamin ministan hasken lantarki Nuhu Wya, ya tabbatar da cewa, akwai yiwuwar farashin amfani da wutar lantarki zai karu a kasar, domin karfafa gwuiwar masu zuba jari su shiga harkar.

Ya kuma ce, karin farashin zai taimaki masu amfani da wutar, saboda za su rage barnatar da wutar lantarki dake wakana a yanzu.

Ba dai bakon abu bane 'yan Najeriya su share makwanni ba tare hasken wutar lantarki ba.

Rashin wutar lantarkin na yin illa ga fannoni daban daban na rayuwar 'yan Najeriya, kama daga masana'antu da sauran sana'oi.

Tuni dai jama'a da dama ke ci gaba da mayar da martani dangane da batun.

Sanata Walid Jibril na kungiyar masu masana'antu ta Najeriya, ya ce suna maraba da wannan garanbawul din ake shirin yi.