Amai da Gudawa a Jihar Katsina

A Jihar Katsina dake Arewacin Najeriya an samu barkewar wata cuta da tayi kama da Cholera wato cutar Amai da Gudawa.

Alkaluman da hukumomin Jihar suka fitar na nuni da cewa wannan cutar ta yadu ne a kananan hukumomi Goma.

Kuma kimanin mutane Chasa'in ne suka rasu, yayinda fiye da mutane dubu daya da dari bakwai ne suka kamu da cutar.

Akan haka ne dai ma'aikatan lafiya na Jihar wadanda ke wani yajin aiki suka koma bakin aikinsu domin taimakawa wajen shawo kan al'amarin.