Watanni shida da juyin mulki a Nijar

Sojojin Nijar

A jamhuriyar Nijar, kungiyar kare hakin dan adam da demokaradiya MONSADEM ta yi kira ga shugaban kasar janar Salu Jibo ya yi wa sabon kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska tun kafin ya kai ga kaddamar da shi, ta yadda dukkan yan kasa za su gamsu da shi.

Haka zalika ,kungiyar ta ce akwai bukatar shugaban kasar ya dubi aikin kwamitin nan da ya kafa domin kwato dukiyar kasa saboda a cewar ta kwamitin na nuna wariya da bambanci.

Kungiyar ta MONSADEM ta yi wadannan kiraye kirayen ne a cikin wata sanarwa da ta fitardon bayyana ra'ayinta game da yadda take ganin al'amura na tafiya watanni 6 bayan da sojoji suka kama mulki a kasar ta Nijar.