Hukumomi a Nigeria sun yi gargadi akan kwalara

Mai fama da cutar kwalara
Image caption Mai fama da cutar kwalara

Ma'aikatar kiwon lafiya a Nigeria ta yi gargadin cewar baki dayan kasar a yanzu haka ta na fuskantar barazana ta barkewar cutar Kwalara.

Ma'aiaktar kiwon lafiyar ta Nigeria ta ce kawo yanzu mutane fiye da dubu shidda da dari shidda ne suka kamu da cutar yayin da 352 suka rasa rayukansu.

Akasari dai cutar ta fi yin kamari ne a yankunan arewacin Nigeriar.

Minista a ma'aikatar kiwon lafiya ta Nigeria, Alhaji Sulaiman Bello, ya ce gwamnati ta tura ma'aikata da kuma magunguna zuwa yankunan da cutar ta barke.

Haka nan gwamnati ta ce ta na kokarin farfado da tsarin nan na duba gari, yadda zaa tabbatar da jamaa suna tsaftace muhallinsu da kuma samar da kyakkawan ruwan sha.