Goodluck ya bayyana sabon shirin samar da lantarki

Layin wutar lantarki
Image caption Layin wutar lantarki

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya bayyana wani shirin da zai ci biliyoyin daloli da nufin gyara bangaren wutar lantarki na kasar mai fama da matsaloli.

A karkashin shirin Shugaba Goodluck Jonathan ya ce kasar za ta sayar da Kamafanin samar da wutar lantarki na kasar kuma ma'aikatansa za su samu hasafin sallama mai tsoka.

A cikin wani jawabi da yayi ga yan jarida da kuma masu fada ajin siyasa na kasar a Lagas, Shugaba Jonathan ya ce kasar za ta dogara a kan kamfanoni masu zaman kansu domin gina sababbin tashoshin samar da wutar lantarki.

Shugaba Jonathan ya ce kasar na bukatar wani juyin juya hali a harkar samar da makamashi a kasar, yana mai alkawarin cewar 'yan Nigeria zasu samu karin hasken wutar lantarki a watan Disamba na shekara ta 2012.

Nigeria na daya daga cikin kasashe masu arzikin Man Petur to amma ta na fuskantar matsalar wutar lantarki.