Kungiya zata sa ido kan aikin samar da kundin zabe a Nijar

Wata mata na kada kuri'a a zaben daya gabata a Nijar
Image caption Kungiyoyin kare hakkin dan adam zasu sa ido kan yadda ake rijistar masu zabe

A jamhuriyar Nijar, hadin gwiwar kungiyoyin kare hakkin dan adam da dimokaradiya wato RODAD,ya kaddamar da wani shiri da nufin sa ido a kan yadda ake gudanar da aikin rijistar sunayen 'yan kasar wadanda suka cancanci jefa kuri'a.

Shugaban hadin gwiwar kungiyoyin,Malam Lawal Tsaibu ya ce kungiyar zata ziyarci dukkanin jihohin kasar a cikin kwanaki hamsin, domin duba yadda aka gudanar da rijistar masu zabe, da kuma yadda ake adana su a cikin na'ura mai kwakwalwa.

Ya kara da cewa yin hakan zai taimaka wajen samar da kundin zabe mai inganci da zai bayar da damar gudanar da zaben da babu magudi a cikinsa. A ranar 11 ga watan maris na 2011 ne dai hukumomin mulkin sojan kasar ta Nijar suke ce za su mika mulki ga sabon shugaban kasa.