Ambaliyar ruwa na ci gaba da barazana a Pakistan

Jama'a da dama sun dogara ne da tallafin abinci daga kasashen duniya
Image caption Jama'a da dama sun dogara ne da tallafin abinci daga kasashen duniya

Ambaliyar ruwa a Kudancin Pakistan na ci gaba da yin barazana ga dubban jama'a, wadanda ya zuwa yanzu suka tsira daga wannan bala'i da ya mamaye yankuna da dama na kasar.

Hukumomi sun kwashe jama'a daga garuruwa da dama na yankin, yayinda suke ta kiciniyar datse ruwan.

Wasu mazauna kauyukan da suka tsere sun nausa sun nufi arewacin kasar.

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce a duk fadin kasar mutane akalla miliyan hudu ne bukatar agajin abinci, har yanzu taimako bai kai gare su ba.