'Yan Taliban sun kai hari a sansanonin NATO

Mayakan Taliban
Image caption Mayakan Taliban

Kungiyar tsaron NATO ta ce, ta fatattaki wasu mayakan Taliban da ke sanye da kakin sojan Amirka, wadanda suka kaddamar da wasu hare-hare biyu a lokaci guda, a sansanonin ta biyu da ke gabashin Afghanistan.

Rahotanni daga yankin sun ce, 'yan Taliban fiye da hamsin ne suka kai hare-haren.

NATOn ta kira jiragen helikopta domin kare sansanonin da ke lardin Khost, kuma ta ce, an kashe maharan akalla 15 a daya daga cikin sansanonin, yayin da kuma a sansani guda aka hallaka masu kai harin su 6.

An kama mahara 5, kuma an gano rigunan bama-bamai irin na harin kunar bakin wake masu yawa.