Bunkasar tattalin arzikin Amurka ta ragu

Mr Ben Bernanke, shugaban babban bankin Amurka
Image caption Mr Ben Bernanke, shugaban babban bankin Amurka

Sabbin kididdiga a Amurka na nuna cewa tattalin arzikin kasar ya karu da kashi guda digo shidda tsakanin watan Aprilu zuwa Yuni na bana, wanda hakan ya gaza hasashen da aka yi da kusan kashi daya cikin dari.

Ana dai ganin cewa ma'aikatar kula da harkokin kasuwancin kasar ta tabbatar da abinda mutane da dama suka sani ne, cewa tattalin arzikin, wanda ya nuna alamun farfadowa a farkon shekarar nan, na yin sassarfa.

Shugaban babban bankin Amurkar, Ben Bernanke ya shaidawa taron shugabanin bankunan kasar cewa a shirye gwamnati take ta dauki matakan tallafawa lamarin.