Kenya ta samu sabon kundin tsarin mulki

Shugaban Kenya, Mwai Kibaki, ya sa hannu akan sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Daga yanzu kenan za a sami babban sauyi kan yadda ake shugabancin kasar.

Shugaba Kibaki ya rattaba hannun ne a lokacin wani kasaitaccen bikin da aka gudanar a dandalin Uhuru, a Nairobi, babban birnin Kenyar, a gaban dimbin jama'a daga ciki da wajen kasar.

Bakin da suka halarci bikin sun hada da shugaba Omar al-Bashir na Sudan, wanda kotun duniya ke nema bisa zargin aikata laifufukan yaki.