Amurka za ta aika da karin helikopta Pakistan

Pakistan Flood
Image caption Ambaliyar ruwa a Pakistan

Amurka ta ce, za ta aika karin jiragen sama masu saukar ungulu goma sha takwas zuwa Pakistan domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa.

Dama dai akwai jiragen sama masu saukar ungulu goma sha uku da Amurkan ta aike zuwa zuwa Kasar.

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa a cikin kwanaki biyu, ambaliyar ruwan da aka yi a kasar ta salwantar da muhallin mutane fiye da miliyan daya a kudancin kasar.

Sannan kuma a wani gari mai suna Thatta dake lardin Sindh mutane fiye da dubu biyu ne suka bar gidajensu ala tilas, saboda ruwan ya kusan mamaye inda suke.

Ruwan da ke Kogin Indus dai ya ninka yawan yanda yake sau arba'in.

Wannan kuma itace ambaliyar ruwa mafi muni da aka yi a yankin, wanda ke kusa da tekun Arabian Sea.