Amurka na duba yiwuwar sake zaburar da tattalin arzikinta

Ben Bernanke, shugaban babban bankin Amurka
Image caption Ben Bernanke, shugaban babban bankin Amurka

Babban bankin Amurka ya ce a shirye yake ya dauki sabbin matakan farfado da tattalin arzikin kasar, bayan da sabbin alkalumma suka nuna cewa, tattalin arzikin bai kai karfin da aka yi hasashe ba.

Tattalin arzikin na karuwa ne da kashi 1 da digo 6 bisa 100 a shekara, watau kusan kashi daya kasa da yadda gwamnatin Amurkan tayi hasashe.

A cewar shugaban babban bankin, Ben Bernanke, mai yiwuwa sabbin matakan su hada da kara yawan kudade a cikin tsarin kudaden kasar, ta hanyar sayen kadarori a kasuwanni.