Matsalar yunwa a Jamhuriyar Nijar

Niger Hunger
Image caption Yunwa a Nijar

A Jamhuriyar Nijar, alamu na bayyana cewa akwai yiwuwar a bana ma a fuskanci matsalar karancin abinci a saboda rashin girbe amfanin gona mai yawa a wadansu sassan kasar.

Al'ummar wani gari mai suna Gidan Basso na fuskantar tashin hankali, ganin yanda yawan ruwan sama ya mamaye gonakin hatsin su.

Tun kimanin shekaru uku da suka gabata ne dai ake fuskantar matsalar noma a garin na Gidan Basso wanda ke da al'umma fiye da dubu biyu.

Wannan kuma ya biyo bayan fuskantar rashin damuna mai kyau.

Mutanen garin sun koka da cewa sam ba sa samun wani taimako daga gwamnati, don haka ne suke yin kira ga hukumomin Nijar din da su agaza musu.