Aman wutar dutse a Indonesia

A tsuburin Sumatra na kasar Indonesia wani dutse ya yi amai a karon farko cikin shekaru fiye da dari hudu.

Wannan lamarin ya tilastawa mutane kimanin dubu goma sha biyu barin muhallinsu.

Tokar da dutsen ke fitarwa dai tasa sararin samaniya ya turnike da hayaki.

Sai dai lamarin bai kai ga dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin saman birnin Maidang dake yankin na Sumatra ba.

Indonesia dai tana daidai wani wuri ne na yankin Asiya dake fuskantar yiwuwar aukuwar aman dutse mai karfin gaske.