Yara a Pakistan na fuskantar barazana

Ambaliyar ruwa a Pakistan
Image caption Ambaliyar ruwa a Pakistan

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya a Pakistan sun ce, kananan yara fiye da dubu saba'in, wadanda tun kafin ambaliyar ruwan da aka yi suna fama da rashin koshi, a yanzu kuma cututtukan da ake dauka ta ruwa, suna barazanar hallaka su.

Jami'in majalisar mai tsara kai agaji a Pakistan din, Martin Mogwanjal, ya ce, a yanzu, yara da yawa, gurbataccen ruwa ne kawai suke sha.

Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su kara yin hobbasa wajen agazawa.

A fadin kasar ta Pakistan, mutane fiye da miliyan takwas sun dogara ne akan kayayyakin agaji a rayuwarsu ta yau da kullum.