Ana gwabza mummunan fada a birnin Mogadishu

Taswirar Somalia
Image caption Taswirar Somalia

An shiga kwana na shidda a yakin da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnatin Somalia da 'yan gwagwarmayar Musulunci, a Mogadishu, babban birnin kasar.

Jami'an lafiya sun ce, fiye da mutane dari sun hallaka, kuma kimanin 230 sun jikkata, tun bayan da masu kishin Islamar suka kaddamar da sabbin hare-hare a ranar Litinin.

Dubban jama'a na tserewa daga Mogadishun, yayin da masu tada kayar bayan ke kokarin kame wata mahimmiyar hanya, wadda ta hada fadar shugaban kasa da filin saukar jiragen saman birnin.

Wani wakilin BBC a birnin ya ce, kimanin tazarar rabin kilomita kawai ta rage tsakanin 'yan tawayen da hanyar, wadda ita ce kawai gwamnatin Somaliyar ke amfani da ita a yanzu haka.