Yajin aikin ma'aikata a kasar Afirka ta kudu

South Africa Strike
Image caption Yajin aiki a Afirka ta Kudu

Shugaba Jocob Zuma na Afurka ta kudu ya yi Allah Wadai da yajin aikin da ma'aikatan kasar ke yi.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin tunawa da wani na gaba-gaba a yaki da mulkin wariyar launin fata, Mista Zuma ya yi fatan cewa bangarorin dake tattaunawa akan yajin aikin za su cimma maslaha.

Bisa ga dukkan alamu dai yajin aikin da ma'aikatan gwamnati fiye da miliyan guda ke yi, zai kara zafi idan aka shiga mako mai zuwa, saboda ma'aikatan hakar ma'adinai ma sun ce zasu bi sahu.