An kubutar Dr Jahlil Balewa daga barayi

Rundunar 'yan sanda Najeriya ta ce ta kubutar da Dokta Jahlil Tafawa Balewa, wani likita wanda aka sace a ranar Juma'ar da ta wuce, a gidan sa dake unguwar Utako, a Abuja.

'Yan sandan sun ce sun sami nasarar kubutar da dokta Jalil din ne da yammacin jiya, a wani daji, bayan sun yi artabu da wadanda ake zargi da sace shi.

Wani jami'in 'yan sandan ya shaidawa BBC cewa sun kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da sace mutumin, suna kuma ci gaba da farautar sauran mutane.