Martanin jihar Bauchi kan cutar kwalara

A Nijeriya, gwamnatin Jihar Bauchi ta kare matakan da take dauka na tunkarar cutar amai da gudawa wadda ta barke a jihar.

Gwamnatin na da maida martani ne kan furucin da kungiyar Red Cross ta jihar ta yi cewa rashin isasshen sinadarin Chlorine da ake tsabtace ruwa da shi na kawo cikas a kokarin magance cutar, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin saba'in.

A halin da ake ciki dai bayanai na nuna cewa mutane kimanin dubu daya da dari bakwai ne suka kamu da wannan cuta a jihar Bauchin.