Aman wutar dutse a kasar Indonisiya

Volcano
Image caption Aman wutar dutse a Indonisiya

Tsaunin Mount Sinabung, da ke tsibirin Sumatra na kasar Indonesiya a yau litinin dinnan ya sake yin aman wuta.

Wannan dai ya sanya kurar toka turnuke sararin samaniya, wanda hakan ya janyo jami'an filin jirgin saman kasar suka dakatar da tashi da saukar jirage a garin Medan.

A baya an dauka cewa tsaunin na Mount Sinabung ba zai taba yin aman wuta ba, tun bayan wadda ya yi a cikin fiye da shekaru dari hudu da suka gabata.

Kwatsam sai aka wayi gari da aman wutar dutse a tsaunin a jiya lahadi.

Wannan al'amari dai ya sanya dubban al'ummar dake kusa da wurin da abin ya faru barin gidajensu.