Mazauna New Orleans na jimamin Katrina

Al'umar New Orleans a Amurka na tunawa da cika shekaru biyar da mahaukaciyar guguwa da ruwa ta Katrina, ta yi ma birnin kaca-kaca tareda halaka mutane kimanin dubu daya.

Shugaba Obama na daga cikin wadanda ke halartar tarukan jimamin.

A yanzu dai kimanin kashi uku cikin hudu ne na al'umar birnin na New Orleans ya koma, yayinda aka gina sabbin matakan kariya daga ambaliyar ruwa.

Sai dai an ce har yanzu wasu anguwannin babu kowa a cikinsu, kuma wasu mutane na korafin cewa an manta da su.