Shakka game da zabe mai inganci a Najeriya

Map of Nigeria
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, wasu masu lura da al'amuran zabe a kasar, sun nuna shakkarsu game da samun zabe me inganci a shekarar 2011.

Sun yi kukan cewa har yanzu ba a samu sauyi a dabi'un 'yan siyasa ba, game da harkokin zabe.

Masu wannan furuci dai na bayyana cewa, duk da ikirarin da wasu ke yi cewa, sun koyi darussa daga zabubbukan da suka gabata da aka yi a kasar, har yanzu abubuwa na nan yanda suke.

Sun dai kara ne da cewa irin abubuwan da suka faru a zabukan-cike gurbin na 'yan majalisar dattawa da aka yi a wasu jihohi a kwanan nan, sun nuna cewa sha`awar aikata magudin zabe ba ta bar zukatan wasu 'yan siyasar ba.

Masu lura da al'amura dai na ganin cewa, matukar ba a samu sauyi ba, to da wuya 'yan Najeriya su cimma burinsu na samun ingantattacen zabe a badi.