Cacar baka tsakanin manyan Jamiyyun Najeriya

Nigeria
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, wata cacar-baki ce ta kaure tsakanin jam'iyyar PDP mai mulki da jam'iyyar adawa ta ANPP.

Wannan dai ya biyo bayan furucin da PDP tayi cewa, irin rigingimun cikin gida dake damun ANPP alama ce ta rashin sanin ciwon-kai, saboda haka jam`iyyar ba ta dace da shugabancin jama`a ba.

Sai dai jam'iyyar ANPP a nata martanin ta zargi PDP da hannu wajen gwara-kan mambobinta da nufin rage mata karfi, ganin babban zaben kasar na karatowa.

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai wani bangare na jam'iyyar ANPP yayi wani taro inda ya tsige shugabannin jam'iyyar bisa hujjar cewa, wa'adin shugabannin zai kare ba tare da an shirya babban taro na kasa don zabar sabbin shugabanni ba.