Pakistan zata sa a binciki zargin zamba

Praministan Pakistan Yousef Raza Gilani, ya ce zai bada umurnin a gudanar da bincike kan zargin da ake yi cewa akwai hannun wasu 'yan wasan kurket na kasar, a wata zamba da aka shirya ta caca.

Ya ce zargin ya sa al'umar Pakistan na ji kamar ta nutse a kasa, domin kunya.

Wata jaridar Birtaniya ta yi zargin cewa an baiwa biyu daga cikin 'yan wasan, Mohammed Amir da Mohammed Asif, kudi domin su karya wasu ka'idojin wasan, a daidai wani lokacin da aka tsara, a lokacin karawarsu da Ingila.

Wasu mutane kan sa makudan kudade domin yin cacar cewa za a yi irin wannan karya ka'ida.

An dai karya irin wadannan ka'idoji, a lokacin karawar, kuma yanzu haka 'yan sandan Birtaniya sun kama wani mutum.