An kaiwa mataimakan gwamnan Bauchi hari

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, an harbi wasu mataimakan gwamna guda biyu, a lokuta dabam-dabam, kuma an ji masu ciwo.

Dukan mutanen biyu, mashawartan gwamnan jahar Bauchi ne, Alhaji Isa Yuguda.

'Yan sanda sun ce lamarin ba shi da nasaba da siyasa, aiki ne kawai na 'yan fashi da makami.

Lamarin ya faru ne, yayin da a baya-bayan nan ake kaiwa 'yan siyasa hare-hare, wanda hakan ke janyo zaman dar-dar, yayin da ake shirye-shiryen gudanar da babban zabe a shekara mai zuwa.