Taron matan kabilar Ibo na shekara-shekara

Mata Kabilar Ibo a taron su.
Image caption Mata Kabilar Ibo a taron su.

Watan Agusta na kowacce shekara lokaci ne da matan al'ummar Ibo a duk inda suke, sukan koma gida don gudanar da wani taro na musamman a kauyukan mazajen aurensu.

Taron wanda sukan kira taron watan Agusta (wato August meeting a Turance), waje ne da sukan tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban kauyukan, da dai sauran matsaloli.

A karshen taron, matan na Ibo sukan yanke shawarwari, tare da bayar da gudunmawa ga kauyukan mazajen nasu. A wannan shekarar, irin wannan taron ya tattaro matan garin Ugwogo Nike, wadanda ke zaune a wurare daban-daban a ciki da wajen jihar, kamar Legas da birnin tarayya Abuja da Fatakwal, har ma da wadanda ke kasashen waje.

Mahimmacin taron

Misiz Uche Ugwu, shugabar kungiyar matan garin na Ugwogo, ta bayyanawa Wakilin BBC muhimmancin taron da cewa: "Taron watan Agusta wani wajen da mata kan hadu ne wuri guda, su tattauna batutuwan da za su ciyar da yankinsu gaba."

Image caption An raba kyautuka a taron

"Kamar a wajen wannan taro namu, muna duba batutuwa da dama wadanda suka hada da batun shigar da 'yan mata kan yi wadda bata dace ba, da rigingimun gonaki da na kasuwa da dai sauransu." In ji Misis Ugwu.

Shugabar matan ta ce, a karshen kowane taro sukan cimma shawarwarin da za su amfani yankinsu. Kuma ta haka, sukan bayar da gagarumar gudunmawa ta hanyoyi da dama: "mun samu nasarar warware matsaloli da dama da 'yan uwanmu ke fuskanta a wasu wurare."

Halartar wannan taro na watan Agusta dai wajibi ne a kan kowacce mace da ke auran dan kabilar Ibo, a cewar Misis Onyiye Onu, wata mata da ta halarci taron: "Idan har mace ba ta halarci taron ba, akwai tarar kudi da za a yi mata, abin da ya kama daga naira dubu biyar zuwa fiye da haka. Muddin kuma mace ta ki biyan tarar, to kayan dakinta za a je a karbe, har sai ta biya tarar a mayar mata."

Sarakunan gargajiya sun bada goyon baya

To, ko ya ya sauran al'ummar yankin na Ibo suke kallon irin wannan kokari da matansu ke yi ? Igwe Ezeogo Linus Mary Ekete, wani basaraken gargajiya a jihar Enugu cewa ya yi:

"Abin da matan ke yi yana da matukar amfani ga jama'armu da 'ya'yanmu. Saboda haka, ina karfafa musu gwiwar ci gaba da wannan hidima. Kuma duk abin da zan iya yi don ganin sun ci gaba da haka, zan taimaka."

Image caption Igwe Ezeogo Linus Mary Ekete, Basaraken gargajiya a Enugu

Galibi dai, akan kwashe tsawon kwanaki hudu zuwa bakwai, ana gudanar da shi wannan taron mata na watan Agusta a sassa daban-daban na yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Masu lura da al'amura kuma na ganin hakan, wani muhimmin abin koyi ne ga takwarorinsu na sauran sassan Najeriya.