Zuma ya nemi a dawo teburin sulhu

Ma'akatan sun nemi karin albashi ne
Image caption Ma'akatan sun nemi karin albashi ne

Shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya bukaci ministocinsa da su farfado da shawarwari tare da kungiyoyin kwadagon kasar, domin shawo kan yajin aikin da ma'aikata ke yi.

Kakakin shugaba Zuman ya ce, sun damu da yadda al'amurra ke rincabewa, don haka akwai bukatar a kawo karshen yajin aikin ba tare da bata lokaci ba.

An sami babban cikas a Afirka ta Kudun, bayan da ma'aikatan asibiti, da malaman makarantu, da kuma sauran ma'aikatan gwamnati fiye da miliyan guda, suka kauracewa ayyukansu.

Da yammacin yau ne ake sa ran komawa teburin sasantawa, tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadagon.