An fara tono mahaka a kasar Chile

Aikin tona rami don ceto mahakan Chile
Image caption Wani ma'aikaci yana duba na'urar da za ta haka ramin da za a ceci mahakan Chile da kasa ta rufe.

Injiniyoyi a kasar Chile sun fara haka rami don ceto mahaka ma'adinai talatin da uku da suke rufe mita fiye da dari bakwai a karkashin kasa tun ranar biyar ga watan Agusta.

Ana sa ran zuwan wadansu kwararru daga Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka (NASA) wadanda suka kware wurin taimakawa ‘yan sama jannati masu zaman kadaici a sararin Subhana domin bayar da shawarwari ga masu aikin ceton.

A yanzu haka dai ana zurawa mahakan abinci da abin sha da sauran abubuwan bukata ta cikin wani bututu kuma sun samu tattaunawa da iyalansu ta wayar tarho.

Sai dai aikin haka ramin ceton nasu zai iya daukar watanni kafin a kammala.