An sako yaron da aka sace a jihar Bauchi

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi a Nijeria ta tabbatar cewa an sako yaron nan dan shekaru sha daya, da wasu mutane suka sace suka yi garkuwa da shi fiye da mako daya da ya gabata.

Rundunar ta ce wadanda suka sace yaron mai suna Mahmud, sun ajiye shi ne a kusa da kamfanin mai na NNPC a Kaduna.

Sai dai rundunar ba ta ce ko an biya wasu kudaden fansa ko kuma a'a ba.

Yanzu haka dai rundunar 'yan sandan ta jihar Bauchi ta mika yaron ga iyayensa, kuma ta ce tana cigaba da bincike don cafke mutanen da suka aikata wannan danyen aiki.