An gurafanar da tsohon ministan Nijar gaban kotu

An gurfanar da tsohon ministan kudin jamhuriyar Nijar, Ali Lamine Zene gaban kotu bayanda aka tsareshi tsawon kwanaki hudu bisa zargin aikata zamba.

An gurfanar da tsohon ministan kudin jamhuriyar Nijar, Ali Lamine Zene, gaban kotu bayanda aka tsareshi tsawon kwanaki hudu bisa zargin aikata zamba.

Lauyan Malam Zene ya ce tshohon ministan ya bayyana a gaban wata kotun majistare, inda daga bisani aka bayar da belinsa.

An kuma umarce shi da ya biya kusan dalar Amurka dubu dari biyu da ake zargin an ba shi a matsayin cin hanci.

Shi dai Malam Ali Lamine Zene ya yi ministan kudi ne na tsawon shekaru bakwai a zamanin mulkin Shugaba Mamadou Tandja, wanda sojoji suka hambarar cikin watan Fabrairu.