Martanin gwamnatin Kano kan zargin Rabo

A Nijeriya gwamnatin jihar Kano da ke arewacin kasar ta mayar da martani a game da zargin yunkurin yin lalata da ake yi wa Darakta janar na hukumar ta ce Fina Finai da dabi'i ta jahar Malam Abubakar Rabo Abdulkarim wanda aka ce an kama shi da wata yarinya mai karancin shekaru a cikin motarsa da daddare.

Wasu rahotanni dai na cewa 'yan sanda ne suka ga wata mota da daddare a wajen da basu amince da shi ba, dalilin ke nan da ya sa suka haskata, inda shi kuma wanda yake cikin motar ya yi kokarin tserewa.

Kuma a cikin wannan haline har ya buge wani mai babur ba kuma tare day a tsayaba, abinda ya harzuka yan acaba suka tare shi tare da kokarin daukar doka a hannunsu, ba dan yan sanda sun shiga tsakani ba, inda kuma a nan ne ta bayyana cewa Malam Rabon shine ke tuka motar.