An bukaci Rwanda ta gyara dokokinta

Shugaba Paul Kagame na Rwanda
Image caption Gwamnatin Rwanda ta amince cewa dokokin na da nakasu

Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta yi kira ga kasar Rwanda ta yi gyara a kan wadansu dokokin kasar guda biyu wadanda kungiyar ta ce ana amfani da su don gallazawa 'yan adawar siyasa da kuma tauye 'yancin fadin albarkacin baki.

A cewar kungiyar ta Amnesty International, an yi amfani da wadansu kalamai a dokokin ta hanyar da za a iya kafa hujja da su don kama masu suka a kan gwamnati, da 'yan adawar siyasa, da 'yan jarida, da kuma masu fafutukar kare hakkin bil-Adama da laifi.

A rahoton da ta fitar, kungiyar ta Amnesty ta ce ma'anar dokokin ta buya ta yadda hatta masana harkar shari'a su kan sha wahala wajen fassara kalmar ‘akidun kisan kare-dangi’.

An sha sukar gwamnatin Rwandan da yin amfani da dokokin don yiwa 'yan adawa takunkumi yayin da ake shirye-shiryen zaben da aka gudanar a watan jiya, wanda Shugaba Paul Kagame ya lashe da kashi casa'in da uku cikin dari na kuri'un da aka kada.

Gwamnatin dai ta ce aiwatar da dokokin wajibi ne don a hana sake aukuwar bakaken kalaman da suka rura wutar kisan kare-dangin da kasar ta fuskanta.

Sai dai a watan Afrilun da ya gabata, gwamnatin ta bayar da sanarawar yin gyaran fuska ga dokokin, wadanda ta amince cewa suna da nakasu.

Ministan Shari'a na kasar ya bayyana cewa gwamnatin za ta fayyace ma'anar kalamomin da ke kunshe a cikin dokokin, to amma kungiyar Amnesty ta ce dokokin na bukatar garambawul cikin gaggawa.