Rwanda za ta janye dakarunta daga Sudan

Kasar Rwanda ta ce tana shirin janye dakarunta dake aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan, muddin Majalisar dinkin duniya ta wallafa wani rahoto dake zargin dakarun Rwanda da hannu wurin kisan kare dangi a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.

Kakakin dakarun Rwanda Laftanar Kanar Jill Rutaremara ya shaidawa BBC cewar dakarun kasar dake Darfur da kudancin Sudan na shirye shiryen ficewa daga yankunan.

Wakilin BBC ya ce daftarin rahoton da majalisar dinkin duniya ta wallafa ya fito, ya zargi dakarun Tutsi na kasar Rwanda, da farauto wa tare da hahharbe 'yan kabilar Hutu da take zarginsu da aikata kisan kare dangi a shekarun 1990 dake gudun hijira a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo.